A cikin sanarwar da Mr. Ban Ki-moon ya bayar, ya nuna al'ajabi game da hare-haren da aka kai, sannan ya yaba game da kokarin sojojin tsaron Somaliya da suka gaggauta na daukar matakan farfado da zaman doka da oda, da goyon baya da tawagar musamman ta AU a Somaliya ta nuna.
Mr Ban ya sake jaddada cewa, zai ci gaba da nuna goyon baya ga gwamnatin Somaliya da jama'arta da su yi kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.
A cikin sanarwar da ta fitar a wannan rana ita ma kwamitin sulhu ta nuna mamakinta game da harin ta'addanci da kungiyar Al-shabab ta kai a ranar 1 ga wata, inda ta jaddada cewa, hare-haren ba za su dakushe anniyar Majalissar wajen goyon bayan jama'ar Somaliya ba. Kwamitin sulhu ya kuma sake jaddada cewa, bisa tsarin kundin mulkin M.D.D., ya kamata a kara yaki da ta'addanci.
A ranar 1 ga wata, an kai hare-haren bom da aka dasa cikin mota har sau biyu a wani otel da ke Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya, lamarin ya haddasa mutuwar mutane a kalla 10. Kungiyar Al-shabab da ke goyon baya kungiyar Al-Qaeda ta dauki nauyin kai wadannan hare-hare. (Bako)