Wata mota mai dauke da bam ta tarwatse sannan aka biyo bayan wannan da jerin luguden harbe harbe a kusa da kofar arewacin fadar Shugaban kasar,abin da Guled yayi bayanin cewa sojojin kasar da taimakon sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar Tarayyar kasashen Afrika AU sun kame magoya bayan kungiyar al shabbab da dama wadanda ake zargin da hannun su a cikin harin.
Manzon musamman na MDD a Somaliya Nicolas Kay wanda ya bayyana a shafin sa na twitter cewa shugaban kasar Hassan Sheik Mohamud na cikin koshin lafiya ya kuma yi allawadai da wannan harin a kan fadar shugaban kasar da ake kira Villa Somaliya. (Fatimah Jibril)