Ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya gana da wasu manyan jami'an kasa da kasa daya bayan daya wadanda suka kawo ziyarar aiki a nan kasar Sin a ran 27 ga wata, wadanda suka hada da Mataimakin Firaminista kana Ministar harkokin waje ta kasar Somaliya Feyziye, Ministan harkokin waje da dunkulewar nahiyar Afrika na kasar Chadi Faki.
Yayin ganawarsa da Madam Feyziye, Wang Yi ya lura cewa, yanzu Somaliya ta samun ci gaba mai armashi wajen shimfida zaman lafiya da raya kasa don haka Sin na fatan farfado tare da kuma yin mu'ammala tsakanin shugabannin kasashen biyu, tare da son kara hadin gwiwa a fannin ciniki da tattalin arziki bisa matakai-matakai, sannan kuma da shiga aikin raya kasar Somaliya.
A nata bangare, Madam Feyziye ta ce, Somaliya na shiga wani muhimmin lokaci ne na samun zaman lafiya da bunkasuwa, kuma Sin sahihiyar kawa ce ga Somaliya, don haka tana fatan Sin za ta bayar da gudunmawarta mai kyau kan aikin shimfida zaman lafiya da raya kasar.
Yayin ganawar tsakaninsa da Mr Faki, Wang Yi ya bayyana cewa, Sin na fatan yin hadin kai da Chadi wajen yin shawarwari da sulhuntawa kan harkokin duniya, ta yadda za su ingiza dangantar dake tsakanin kasashen biyu zuwa gaba. A nashi bangaren kuwa Mr Faki ya mika godiyar kasar a Chadi bisa ga taimakon da Sin ta bata ba tare da ko wani sharadi ba, don haka kasar na fatan zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu a dukkan fannoni. (Amina)