Ina ganin Somaliya na samun ci gaba bisa hanya ta kwarai a yanzu kuma shekara mai zuwa za mu dukufa wajen aiki tare da gwamantin tarayya na kasar Somaliya da kuma kungiyoyin shiyya shiyya, in ji mista Hailemariam a gaban 'yan jarida.
Hakazali ya kara da cewa kasar Habasha na kasancewa wani jigo ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Somaliya, sannan kuma sojojin kasar Habasha za su ci gaba da tallafawa tawagar zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika (AMISOM) da rundunar sojojin Somaliya. Sojojin Habasha za su ci gaba da tsayawa kasar har sai sun tabbatar da cewa mayakan kungiyar Al-Shebab ba za su kasance tamkar wata barazana ga shiyyar musammun ma a kasar Somaliya ba, in ji mista Hailemariam.
A cewar faramanistan Habasha, ta'addanci matsala ce ta duniya domin haka ya kamata a daidaita ayyuka tare da mutane da kuma kungiyoyin da abun ya shafa wajen yaki da ta'addanci.
Bisa ga haka muna tuntubar juna yadda ya kamata da kasashe makwabta, har ma da kasar Kenya, kuma muna aiki tukuru domin daidaita ayyukanmu ta yadda irin harin ta'addanci da aka kai a birnin Nairobi na kasar Kenya ba zai sake abkuwa ba a wannan shiyya. (Maman Ada)