Wani rahoton sa ido na hadin gwiwa na reshen nazari na kungiyar FAO kan tsaron abinci da cibiyar harkar abinci ta kasar Somaliya (FSNAU) ya tabbatar da cewa kusan mutane dubu 857 za su bukaci agajin abincin gaggawa, bisa wani hasashe.
Watan Mayu ya kasance wani lokaci mai tsanani da za'a fuskanta idan aka rasa ruwan sama da kuma cigaban rashin tsaro, wani yanayin matsalar da ba'a taba gani ba a cikin yankunan kudancin kasar Somaliya da ma cikin wasu yankunan arewa maso gabashin kasar, da ta kasance shiyyar da aka fi kiwon dabbobi in ji Daniel Molla, babban kwararre na cibiyar FSNAU. (Maman Ada)