Kamar yadda wani da ya gane ma idanun sa ya yi bayani,ya ce da sanyin safiyar talatan nan din hakan ya faru kuma da ganin harin musamman aka shirya shi domin wannan otel din dake dauke da dakarun wanzar da zaman lafiya na gwamnatin Somaliya da AU.
Maharan da fari sun yi amfani da kai harin kunar bakin wake sannan daga baya wadansu masu dauke da manyan makamai suka fada ma sojojin wajen da fada sai dai kamar yadda Yusuf Hasey Kakakin rundunar sojin gwamnatin yayi bayani ma kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua an samu nasara akan 'yan kungiyar abinda yasa aka kashe da daman su sauran kuma da suke tseren an bisu domin a kamo.
Kungiyar masu tsatsauran ra'ayin islama Al Shabbab a nan take ta dauki alhakin harin na otel din tana ikirarin cewa tayi nasaran kashe sojoji da dama. (Fatimah Jibril)