in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaro na MDD ya yi alla wadai da harin ta'addanci kan wani ginin otel a Somaliya
2014-03-20 11:13:50 cri
Kwamitin tsaro na MDD ya yi tir da alla wadai a ranar Laraba da babbar murya kan harin ta'addanci na baya bayan nan da aka kai wa wani ginin Otel a Somaliya, tare da bayyana cewa duk wani harin ta'addanci babban laifi ne da rashin hujja.

Mambobin kwamitin tsaro sun yi alla wadai da harin ranar jiya kan ginin Otel Bula Burde dake kasar Somaliya da kungiyar Al-Shabab da dauki alhakin kai wa, in ji wata sanarwa da kwamitin ya fitar a ranar Laraba da yamma.

A ranar Talata ce, wani dan kunar bakin wake ya kutsa mota makire da boma bomai a cikin ginin Otel Bula Burde, tare da kashe mutane da dama.

Kungiyar Al Shabab ta kai wasu jerin hare hare domin mai da martani kan sabon samamen da dakarun kungiyar tarayyar Afrika AU suke kai wa da nufin karbe sansanonin mayakan Al -Shabab. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China