Bayan abkuwar hadarin, sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar AU dake kasar Somaliya sun bayar da wata sanarwa, inda suka ce, wannan jirgin sama ya fadi ne yayin da yake kokarin sauka a filin jiragen sama da karfe 8 na safiyar ranar 9 ga wata, daga baya ya yi fashe. Sojoji 4 dake cikin jirgin saman sun mutu, kana sojoji biyu sun ji rauni. Yanzu ana yin bincike kan dalilin aukuwar hadarin.
Wani jami'in filin jiragen sama na Mogadishu ya bayyana cewa, wannan jirgin saman yana dauke ne da makamai daga kasar Habasha. Watakila kungiyar AU ko sojojin gwamnatin kasar Somaliya sun mallaki wadannan makamai ne, domin yin yaki da dakaru masu adawa a kasar wato Al Shabaab. A halin yanzu, sojojin kasar Habasha ba su shiga aikin kiyaye zaman lafiya na kungiyar AU dake kasar Somaliya ba, amma sun dade suna bada gudummawa ga gwamnatin kasar Somaliya wajen yaki da kungiyar adawa ta Al Shabaab.
Sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar AU dake kasar Somaliya sun bayyana cewa, babu illa ga hanyoyin tashi da sauka na filin jiragen sama na Mogadishu, amma yanzu an rufe filin jiragen saman. Ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Somaliya ba ta bayyana ra'ayinta ba dangane da wannan lamari. (Zainab)