Shugaban majalisar gudanarwa ta kungiyar tarayyar kasashen Turai ta EU Von Rompuy da shugaban majalisar mambobin EU Manuel Durao Barroso sun aikawa shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta wata wasika a jiya Litinin 23 ga wata, inda suka bayyana fatan yin hadin kai da kasar Kenya domin yaki da ta'addanci, da kuma murkushe kungiyar masu tsattauran ra'ayin Islama ta kungiyar matasan Somaliya ta SYP, domin shimfida zaman lafiya da karko a kasar Somaliya, ta yadda 'yan gudun hijira za su koma kasarsu da sauri.
Ban da haka, shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya nuna a wannan rana cewa, akwai alamar yaduwar SYP a duniya, ba ma kawai abin zai kawo babbar illa ga nahiyar Afrika ba har ma ga dukkan duniya don haka gwamnatin kasar Somaliya tana dukufa kan murkushe SYP bisa karfinta yadda ya kamata. (Amina)