Sanarwar ta ce, babban sakatarenya kuma jajantawa iyalan wadanda suka mutu a sakamakon farmaki, tare da fatan ganin wadanda suka jikkata za su warke cikin sauri. Ban da haka, ya kuma yi yabo ga ma'aikatan MDD da ke Somaliya game da yadda suke ci gaba da ba da taimako duk da mawuyacin halin da suke ciki. Ban Ki-moon ya ce, zai nuna tsayayyen goyon baya ga gwamnatin kasar Somaliya, don ganin ta hukunta masu laifi tare da hana kara aukuwar al'amura irin wadannan, kuma a cewarsa MDD ba za ta sauya niyyarta ta marawa jamar Somaliya da gwamnatin kasar baya ba.
Har wa yau, wakilin musamman na babban sakataren da ke kasar Somaliya da ma wakilin musamman na kungiyar tarayyar Afirka da ke kasar su ma sun yi Allai wadai da farmakin.
Harin dai na ranar 13 ga wata da aka kai kan ayarin wasu motoci a wajen fikin jirgin sama na Mogadishu, ya hallaka a kalla mutane shida suka hallaka, a yayin da wasu da dama suka ji raunuka, tuni kuma kungiyar al-Shabaab ta yi shelar daukar alhakinsa.(Lubabatu)