Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Somaliya ya bayar, an ce, an kai farmaki kan wata mota ta jirgin sama maras matuki a garin Jilib da ke kudancin kasar Somaliya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mambobin kungiyar Al Shabaab guda biyu, ciki har da wani babban kamandan kungiyar din.
Wani da ya ganewa idonsa lamarin da ya bukaci kada a saka sunansa ya ce, bayan farmakin, dakarun kungiyar Al Shabaab sun isa wurin domin daukar gawawwakin mambobinsu. Mutumin ya kara da cewa, lallai babban kamandan da aka harbe har Lahira maji'in kungiyar ne dake kula da ayyukan kai farmakin kunar-bakin-wake.
A halin yanzu gwamnatin Somaliya ba ta ce kome ba kan wannan lamarin.(Danladi)