Daga bakin ranar 9 ga watan Afrilu, akwai 'yan gudun hijirar kasar Somaliya 956066 da aka tsugunar da su musammun ma yankunan kasashen Kenya, Yemen, Masar, Habasha, Ereathria, Djibouti, Tanzania da kuma Ouganda kana fiye da miliyan 1 da dubu dari 1 'yan Somaliya aka kaurar da su a cikin kasar musammun ma zuwa yankunan Kudu maso Tsakiyar kasar, in ji wannan hukuma.
Adadin 'yan gudun hijirar Somaliya dake kasar Kenya an kiyasta shi zuwa dubu dari biyar kuma wannan adadi yana karuwa bisa dalilin tashe tashen hankali da matsalar fari dake kamari a wannan shiyya dake kusurwar Afrika wanda yake tsakanin bangarori masu gaba da juna suka rugurguza tun daga bakin shekarar 1991, koda yake a baya bayan nan kasar ta fara kama hanyar zaman lafiya da kwanciyar hankali. (Maman Ada)