in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kasashen waje dake Somaliya sun kai samame a wani gidan dake hannun 'yan kungiyar Al-Shebab a Barawe
2013-10-05 16:16:41 cri
Wani rukunin sojojin kasashen waje dake kasar Somaliya sun kai samame a wani gidan dake hannun 'yan kungiyar Al-Shebab dake birnin Barawe dake kuduncin kasar Somaliya a cewar wani mazaunin wannan yanki.

Mun rika jin karar harbin bindigogi tsakanin sojojin kasashen waje dake Somaliya da mayakan kungiyar kishin Islama ta Al-Shebab a cikin gidan , in ji wannan mazauni a yayin da yake hira ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Sojojin kasashen wajen dake Somaliya sun kai wani hari ta ruwa ta wannan birnin dake bakin teku in ji wannan mutumin da ya bukaci a sakaya sunansa, wanda kuma ya bayyana cewa har yanzu ba'a da wani adadin yawan mutanen da suka mutu ko suka ji rauni.

Harin dai ya biyo bayan wani gungun dakaru dake da alaka da kungiyar Al-Qaida ya sanar da alhakin kai hari a cibiyar kasuwancin Westgate dake birnin Nairobi a makonni biyu da suka gabata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China