An kaddamar da dandali mai zaman kansan al'umma karo na uku tsakanin Sin da Afrika a kasar Sudan
An kaddamar da dandalin al'umma mai zaman kansa karo na uku tsakanin Sin da Afrika a Khartoum na kasar Sudan a ranar litinin 12 ga watan nan mai Wakilai wakilai kimanin 200 da suka fito daga kasar Sin da kasashen Afrika 27. Wakilan za su tattauna kan jigon "Koyi daga junaKoyon dabaru da fasaha, zurfafa hadin gwiwa da daukan daukar matakai da suka dace domin taimakawa jama'ar bangarorin biyu wajen kawar da talauci gaba daya", inda kuma zasu yi musanyar ra'ayi kan yadda za su dauki mataki mai amfani cikin hadin kai domin baiwa jama'a damarr cin gajiyarsa.
Mataimakiyar shugaban kwamiti mai ba da shawara kan harkokin siyasa karo na 11 kuma mataimakiyar shugabar kungiyar mu'ammala tsakanin kasa da kasa na kasar Sin Madam Wang Zhizhen ta karanta sakon fatan alheri daga shugaban kasar Sin Xi Jinping, iInda ta bayyana cewa, a cikin shekaru uku da suka gabata, wannan dandali ya baiwa kungiyoyi masu zaman kansun jama'a daga bangarorin biyu wani mataki mai kyau wajen koyi daga juna kan dabaru da darussafasahohi, da hadin kai tare kama gami da tsai da tsare-tsaren nan gaba. (Amina)