Bisa rahoton wani binciken da aka yi, yawancin 'yan Afrika na ganin cewa, jarin da Sinawa suka zuba a nahiyar Afrika na ba da gudunmawa wajen samar da guraben ayyukan yi a kasashen.
Wannan bincike mai taken "Ra'ayin 'yan Afrika game da jarin da Sinawa suka zuba a nahiyar Afrika", wanda aka gudanar a kasashen Afrika 15 a bara, karkashin taimakon wani shafin yanar gizo, na kungiyar sana'ar kere-kere ta kasar Kenya, ya nuna cewa, yawancin 'yan Afrika na maraba da jarin da Sinawa ke zuba.
A cikin wadannan kasashe da aka yi bincike, mutane kaso 75 bisa dari na ganin cewa, jarin da Sin ta zuba na da amfani sosai.
Ya zuwa yanzu, Sin ta zama kasa mafi girma, dake zuba jari a nahiyar Afrika. Yawan kudin hada hadar cinikayyar dake tsakanin Sin da Afrika ya karu daga dala biliyan 10 zuwa dala biliyan 200, tsakanin shekarar 2010 zuwa shekarar 2013. (Amina)