Rukunin samun ci gaban Afrika ya ba da wani rahoto mai taken "Ci gaban Afrika a shekarar 2014" a taron kolin Afirka na dandalin tattalin arzikin duniya karo na 24 a ran 8 ga wata, inda aka yi kira ga shugabannin kasashen Afrika da su dauki matakan da suka dace domin kawar da nuna bambanci da rashin daidaituwa.
Shugaban wannan rukuni, kuma tsohon babban magatakardan MDD Kofi Annan ya bayyana yayin da ya gabatar da rahoto cewa, ban da alkawarin cimma wasu manyan muradun da kasashe daban-daban suka yi yayin da suka daddale sabbin yarjeniyoyin raya duniya gaba daya, kamata ya yi, su yi alkawarin rage gibin da ke tsakanin masu wadata da matalauta, da kauyuka da birane, maza da mata.
Dadin dadawa, rahoton ya mai da hankali sosai kan raya sha'anin aikin gona, a ganin Annan kasashen da suke dogaro da sha'anin gona kamar Habasha da Ruwanda, sun riga sun shaida cewa, wannan sha'ani tamkar wani mataki ne mai karfi wajen samun bunkasuwar tattalin arziki da al'umma baki daya da rage talauci. (Amina)