Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Hong Lei ya bayyana a Talata nan 21 ga wata cewa, Sin na fatan hadin kai da kasashen duniya domin ba da gudunmawar ta wajen shimfida zaman lafiya da tabbatar da tsaro da bunkasuwar Afrika ta tsakiya cikin lokaci. Yayi bayanin cewa, yadda aka zabi sabuwar shugabar wucin gadi a kasar ya zama muhimmin mataki wajen kyautata halin da kasar ke ciki, a don haka Sin na maraba da wannan.Kakakin ya ce har ila yau kasar Sin na fatan cewa, bangarori daban-daban dake da alaka da wannan batu za su dauki matakan da suka dace karkashin jagorancin sabuwar gwamnatin wucin gadi, domin kawo alheri ga kasa da jama'arta, ta yadda za a hada kan al'umma da kyautata halin tsaro da jin kai da kasar ke fuskanta, hakan in ji shi zai samar da wani yanayi mai kyau ga ayyukan sauyin jagoranci a kasar da sake raya ta. (Amina)