in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kiran kasashen yammacin Afrika da su gaggauta kudurin kasuwancin makamai
2014-04-05 16:03:53 cri
Kungiyar dake kula da kananan makamai a yammacin Afrika(RASALAO) ta yi kiran gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS data gaggauta kudurin da ya shafi kasuwancin mamakai (TCA), da MDD ta amincewa a ranar biyu ga watan Afrilun shekarar 2013.

Ya zuwa ranar hudu ga watan Afrilun shekarar 2014, kasashe 31 inda a cikinsu kasashen kungiyar ECOWAS biyu wadanda suka hada da Mali da Najeriya kawai suka ajiye takardun rattaba hannu kan kasuwancin makamai, in ji madam Mariam Liehoun shugabar RASALAO reshen kasar Burkina-Faso cikin damuwa a yayin wani taron menama labarai a ranar Jumma'a a birnin Ouagadougou.

Ta kara da cewa Burkina-Faso ta rattaba hannu kan kudurin a ranar 18 ga watan Maris, amma kuma har yanzu bata ajiye takardunta a MDD ba.

A cewar madam Liehoun, kasashe 116 cikin 193, yawanci kasashen Afrika sun rattaba hannu kan dokar TCA, amma kuma babban kalubalen da ake fuskanta yanzu shi ne rattaba hannun kan dokar baki daya cikin gaggawa.

Baffour Amoa, shugaban RASALAO ya bayyana a nasa bangare cewa an gudanar da ayyukan fadakarwa zuwa ga hukumomi da al'ummomi a wannan fanni, tare da kare cewa kungiyarsa ta kaddamar tun cikin watan Janairun shekarar 2014 wani rangadi domin bada Karin haske kan dokar TCA. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China