Kudurin ya bukaci da a kara inganta ayyukan ofishin da suka hada da taimaka wa yunkurin kafa gwamnatin wucin gadi ta kasar, taimakawa kawo karshen zubar da jina, samar da agajin jin kai ga kasar, da kuma taimakawa sabbin hukumomin wajen tafiyar da harkokin kasa domin bada hidima mai kyau ga jama'a, tare da tabbatar da tsaro da kare hakkin dan Adam a wannan kasa dake tsakiyar Afrika.
Kudurin ya dora muhimmanci sosai game da halin tsaro dake ci gaba da tsananta, da rashin doka, inda aka dora muhimmanci sosai kan mummunan tasirin da rikicin jamhuriyar Afrika ta tsakiya ke kawo wa shiyyar tsakiyar Afrika da sauran yankunan. Haka kuma, kudurin ya yi kira ga gwamnatin wucin gadi da ta sauke nauyin dake wuyanta, da kokarin samar da zaman lafiya da sulhuntawa tsakanin kabilun kasar.(Bako)