Hanyar gargajiya ta samun kudade ta nuna iyakarta, musammun ma hanyoyin da suke da nasaba da kungiyoyin kasa da kasa da muka sani har zuwa yanzu. Lokaci yayi mu nemi wasu sabbin hanyoyin samun kudi ta hanyar dangantaka tsakanin gwamnati da masu zaman kansu da zata iyar kawo karin kudade da ya kamata a zuba a nahiyar Afrika in ji mista Doucoure tare da byayyana cewa idan ana son a cimma mafita, to ya kamata Afrika ta rika samun a kalla dalar Amurka biliyan 45 a kowace shekara.
Haka kuma jami'in ya jaddada cewa ba'a baiwa ayyukan gine gine samar da ruwan sha muhimmaci sosai a Afrika ba, musammun daga wajen gwamnati, inda aka fi maida hankali ga sufuri, wasannin motsa jiki da sadarwa.
Yawancin lokaci idan aka ambaci batutuwan gine gine sai a rika tabo maganar batun hanyoyi, filayen jiragen sama amma sai ana rika mantawa da muhimman gine gine da suka shafi ruwa da tsabta. (Maman Ada)