Oscar Pistorius mai shekaru 27 a duniya, kana shahararen dan tseren nakasassa. Ana tuhumarsa da laifin kashe budurwarsa,inda za a yanke masa hukunci a ran 3 ga watan Maris.
Babbar kotun kasar ta yanke shawara a jiya Talata 25 ga wata cewa, ta yarda da rokon da wasu kafofin yada labarai suka yi na neman a watsa shari'ar da za a yi masa kai tsaye ta Talabijin, amma ba ta yarda a dauki hoton bidiyon Oscar Pistorius da masu kare shi ba da sauransu,yayin da su kuma gidajen rediyo aka amince musu su watsa sautin zaman kotun.
Kafofin yada labarun kasar na ganin cewa, watsa shari'ar kai tsaye ta kafofin wtasa labarai zai taimaka wajen yanke hukunci cikin adalci. Amma lauya dake kare Oscar ya ce, wannan mataki katsalandan shari'a ne ga wanda ake tuhuma.(Amina)