Rahoton yace karuwan tattalin arzikin a nahiyar ana ganin zai habaka saboda taimakon tattalin arzikin duniya da hada hadar yanayin kasuwanci na shiya shiya sannan farashin manyan ababen bukata zai inganta,matsin wajen samar da ababen more rayuwa kuma zai sassautu, za'a kuma samu karin dangantaka na ciniki da zuba jari da kasashen da tattalin arzikin su ke tasowa.
Sai dai kuma rahoton ya nuna cewa saurin karuwan tattalin arzikin da nahiyar Afrika ta samu yanzu zai danganta ne bisa ga kayayyakin masarufi da kuma kayayyakin da aka fitar zuwa kasashen waje,amma kuma duk da haka bai kai yadda ya kamata ba a nahiyar.
Karuwar tattalin arzikin inji rahoton ya kasa cimma burin samar da ayyukan yi da fadada cibiyoyin tattalin arziki da walwalar al'umma da ake bukata domin rage radadin talauci da cike gibin da ake da shi a kasashe da dama.(Fatimah Jibril)