in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mamphela Ramphel ta bayyana niyyarta na shiga zaben shugaban kasa a matsayin 'yar takarar adawa a kasar Afrika ta Kudu
2014-02-03 16:29:11 cri
Mamphela Ramphel, maifafutukar yaki da wariyar launin fata da ta yi fice, ta dawo kan wata yarjejeniyar domin shiga takarar zaben shugaban kasa mai zuwa a matsayin 'yar takarar kawancen jam'iyyun adawa na DA, a cewar wannan kawancen a ranar Lahadi.

Matakin da madam Mamphela Ramphel ta dauka na dawowa kan wannan yarjejeniya wani ja da baya ne ga demokaradiyya a kasar Afrika ta Kudu, in ji shugabar kawacen DA, madan Helen Zille.

Kwamitin zartaswa na DA ya yi wani taron gaggawa a ranar Lahadi tare da madam Ramphela domin cimma matakan dake cikin wannan yarjejeniya dake nuna cewa mai yaki da wariyar launin fatar za ta iya shiga takarar zaben shugaban kasa mai zuwa a matsayin 'yar takarar DA.

A yayin wannan ganawa, madam Mamphela ta sake dawowa kan wannan yarjejeniya, in ji madam Zille.

Madam Mamphela ta ba da sanarwa a kwanakin baya cewa ta amince da gayyatar DA ya yi mata na tsaya wa takara a zaben shugaban kasa na shekarar 2014.A cikin watan Junin shekarar 2013, madam Mamphela ta kafa sabuwar jam'iyyarta mai sunan Agang SA domin fafatawa tare da jam'iyyar ANC mai mulki a zabubukan masu zuwa a shekarar 2014.  (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China