in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya yi kiran Afrika da ta rage talauci da kafa guraben ayyukan yi
2014-01-29 10:08:43 cri
A ranar Talata ce, bankin duniya ya yi kira ga kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara da su samar da guraben ayyukan yi masu alfanu da kuma kawar da talauci domin ingiza samun cigaban tattalin arziki.

Babbar hukumar kudi ta duniya ta nuna cikin wani rahotonta na baya kan aikin yi ga matasa a Afrika cewa, kafa guraben ayyukan yi bisa albashi mai kyau ga matasan nahiyar na da babban muhimmanci domin cigaban tattalin arzikin wannan shiyya.

Mataimakin shugaban bankin duniya dake kula da harkokin shiyyar Afrika, mista Makhar Diop ya bayyana cewa janyo hankalin masu zuba jari a cikin manyan kamfanoni masu samar da guraben ayyukan yi da ba da albashi mai tsoka a cikin tattalin arzikin kasa na raya kasa, amma wannan wani bangare kawai na mafita na kalubalen matsalar samu aikin yi na matasan Afrika. Ga miliyoyin matasan Afrika da neman mafita ta hanyar gudanar da kananan ayyukan boye, dole sai an tabbatar da ba su damar ga samun filaye, horar da su da kuma ba su jari, in ji mista Diop.

Rahoton shiyyar mai sunan "Aikin yi ga matasan dake kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara" na nuna cewa, kusa da kashi 80 cikin 100 na sabon jini za su cigaba da aiki a cikin kananan gonaki da gidaje a cikin gajeren lokaci mai zuwa. Tare de fiye da yawan al'umma wannan shiyya dake kasa da shekaru 25, kusan matasa miliyon 11 na Afrika za su shiga kasuwar aiki a ko wace shekara a tsawon karni mai zuwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China