A yayin wani taron manema labarai a ranar Talata a lokacin babban taron tarayyar Afrika karo na 22 a cibiyar kungiyar dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha, kwamishinar ta nuna cewa kasar Sin ta taimakawa nahiyar Afrika sosai musamman ma a fannonin gine-gine, lamarin da ta bayar da muhimmancin gaske ga raya kasuwanci tsakanin kasashen Afrika da kuma bunkasa aikin noma a nahiyar.
Kasar Sin na daya daga cikin abokan huldar da kungiyar AU take fadada dangantaka a fannin noma, in ji madam Rhoda Peace.
Afrika na karuwa sosai daga kasar Sin musammun ma ta fuskar noma, bayan kuma tana taimakawa bunkasa gine-ginen ayyukan more rayuwa a yawancin kasashen Afrika, haka kuma kasar Sin tana zuba jari a cikin kamfannonin sarrafa albarkatun gona ta hanyar bangaren kamfannoni masu zaman kansu, in ji wannan jami'a. (Maman Ada)