Kwamishinar ta lura cewa, kasar Sin tana ayyukan a zo a gani na cigaba da suka hada da shimfida hanyoyin mota da layin dogo, gadoji filin saukar jiragen sama, filin wassannin motsa jki a cikin sauran ayyukan da take yi.
Elham Mahmoud Ibrahim ta ce, yadda Sin take gudanar da manyan ayyukan ta a kasashen Afrika, haka take aiwatarwa a yankuna da shiyya shiyya wadanda suka taimaka kwarai wajen ayyukan samar da ababen more rayuwa a nahiyar, wato PIDA.
A cewar Kwamishinar, zuba jari na daya daga cikin kalubale na kayayyakin cigaba a Afrika. Ya ce kalubalen su ne ababen more rayuwa ba su isa ba kuma ba su da inganci. Don haka akwai bukatar a zuba jari sosai. (Fatimah Jibri)