John Ging, darektan ayyukan cibiyar daidaita harkokin agaji ta MDD (OCHA), ya shaida wa manema labara cewa dakarun sa kai na kristoci dana musulmai za su kara zafafa wutar gaba tsakanin kabilun kasar, kana kuma mutanen sun yi watsi da imaninsu wajen kara zafafa wutar kiyayya da tashe tashen hankali da ba'a taba ganin irinsu ba.
Mista Ging, da ya dawo daga garin Boda dake kudancin kasar Afrika ta Tsakiya, ya bayyana cewa ya kuma kara nuna damuwarsa kan wani sabon abun tashin hankali, wato al'ummar Afrika ta Tsakiya na zargin yanzu kristoci da musulmai, maimakon nuna yatsa ga gungun kungiyoyin dake dauke da makamai kamar yadda suke a da. (Maman Ada)