Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a safiyar ranar Asabar 10 ga watan nan. Yayin ganawar ta su Mr Li ya bayyana cewa, a cikin shekaru fiye da 50 da suka gabata, tun bayan kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, dangantakar dake tsakaninsu na samun bunkasuwa yadda ya kamata, duk kuwa da wasu kalubalolin da aka fuskanta.
A nasa bangare, Mr Kenyatta a madadin gwamnatinsa da jama'ar kasar ta Kenya, ya taryi Mr Li cikin farin ciki kwarai, ya na mai cewa wannan ziyara da Mr Li Keqiang ya gudanar, a daidai wannan lokaci na cika shekaru 50 da ziyarar tsohon firaministan kasar Sin marigayi Zhou Enlai a Afrika, za ta kara sa kaimi ga zurfafa sabuwar dangantakar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu.
Dama dai a bara ma sai da shugaban Kenyatta ya kawo ziyarar aiki nan kasar Sin, ziyarar da ta sanya shugaban kasar Sin karfafa matsayin kasashen biyu a fannin huldar su zuwa wani sabon matsayi. Matakin da kuma ya bada damar fadada dangantakar aminci da siyasa, da moriyar juna, da hadin kai tsakanin sassan biyu.
Har ila yau kasar Sin na fatan kara amincewa juna tsakanin shugabannin biyu a siyasance, da taimakon juna kan wasu manyan batutuwa dake da alaka da cimma moriyarsu, ta yadda za a ingiza dangantakar dake tsakaninsu gaba.
Yayin dai waccan ziyara ta Mr Li a Kenya, ya gana da direktan gudanarwa, na hukumar tsara shirin kare muhalli na MDD wato UNEP Mr Achim Steiner, da direktan gudanarwa na hukumar kula da zaman rayuwar Bil Adam ta MDD Joan Clos a birnin Nairobi.
Dadin dadawa, bisa rakiyar mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto, Mr Li ya kai ziyara wani lambun shan iska dake Nairobi, wurin da aka kone wasu tarin hauren giwa, domin nuna goyon baya ga yakin da ake yi da farautar namun daji ba bisa ka'ida ba, da haramtacciyar sana'ar nan ta fasakwaurin hauren giwa, inda Mr. Li yayi jawabin amincewa da daukar wanan mataki.(Amina)