A cikin wata sanarwar da ya bayar, mista Kerry ya bayyana cewa, sun samu bayanan dake nuna cewa akwai wasu shugabannin kasar dake rufe ido game da yunkurin farfado da zaman lafiya, a maimakon haka, suna cigaba da nuna goyon baya ga wasu mayaka domin kara zafafa wutar rikici, lamarin dake daukar hankalin gwamnatin kasar Amurka kwarai.
Bugu da kari, Kerry ya kalubalanci shugabar wucin gadin kasar da tsoffin shugabannin kasar da su yi kira ga magoyansu da su daina kai hare hare ko amfani da karfin tuwo kan fararen hula. Ban da haka, ya yi kira ga kasashe makwabta da su daina taimakawa dakarun kasar Afrika ta tsakiya da makamai da makamantan haka. (Amina)