A gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Alhamis a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mr Qin Gang ya bayyana ra'ayin kasar Sin na kalubalantar Amurka da kada ta yi amfani da ma'auni iri biyu kan batun yaki da ta'addanci, da kaucewa samar da sako bisa kuskure ga kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi, kamata ya yi ta dauki matakin da ya dace domin kiyaye hadin kai da kasashen duniya ke yi na yaki da ta'addanci.
Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne wasu 'yan ta'adda suka kai hari a jihar Xin Jiang, inda mataimakin kakakin majalisar gudanarwa ta Amurka ta yi kira ga kasar Sin da ta samarwa jama'arta hakkin fadin albarkacin baki, tare da fatan ma'aikatar tsaron lafiyar jama'a za ta yi hakuri. An aza tambaya cewa, mene ne ra'ayin da Sin ke dauka kan wannan batu.
A nasa bangare, Mr Qin ya jaddada cewa, akwai shaidun dake tabbatar da cewa, babu shakka wannan ayyukan ta'addanci ne. Idan an kai irin wannan hari a Amurka, in ji Mr Qin, yaya gwamnatin Amurka da jama'arta za su mai da martani game da irin wannan kalami da mataimakin kakakin majalisar gudanarwa na Amurka ta yi. (Amina)