Har wa yau game da bayanin shugaban kasar Amurka Barack Obama na cewa, kasar ta yanke shawarar daukar matakan soja kan kasar Syria, Hong ya furta cewa, kasar Sin ta dade tana mai da hankali kan yanayin Syria, kuma tun asali tana ganin cewa, ba za a iya daidaita batun Syria ba sai dai ta hanyar siyasa. Sin ta mai da hankali sosai kan yiwuwar daukar matakan soja kan kasar Syria da wasu kasashe za su yi. Kamata ya yi kasa da kasa su bi kundin tsarin mulkin MDD da ka'idojin dangantakar kasashen duniya yayin da suke daukar matakai, a kokarin kauracewa tsanantar yanayin da ake ciki a Syria, da kara kawo illa ga yankin Gabas ta Tsakiya.(fatima)