Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying yau Alhamis 1 ga wata ta bayyana cewa, kasar Sin ta nuna rashin yarda karara da kudurin da majalisar dattijai ta kasar Amurka ta zartas kan batun da ya shafi yankin takun da ke kudanci da gabashin kasar Sin, kuma ta bayyana wa Amurka rashin jin dadinta.
A ranar 29 ga watan jiya ne, majalisar dattijai ta kasar Amurka ta zartas da wani kudurin da ba ya da tasiri a karkashin dokokin kasar, inda aka bayyana cewa, Amurka na goyon baya da a warware rigingimun da suka shafi yankuna da ikon mallakar fadin tekun Asiya da Pasific cikin lumana. Wannan tamkar nuna wa kasar Sin matsin lamba ne a kan batun yankin tekun da ke kudanci da gabashin kasar.
Game da wannan, Madam Hua ta bayyana cewa, 'yan majalisar dattijan sun gabatar da wannan daftarin kuduri ne ba bisa hakikanin tarihi ba, har ma sun zargi kasar Sin ba bisa wata hujja ba, lallai wannan ba daidai ba ne. Don haka kasar Sin ta nuna rashin yarda da kudurin da babbar murya, da kuma bayyana wa Amurka rashin jin dadinta.(Kande)