in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron tattaunawa karo na 4 game da musayar al'adu a tsakanin kasashen Sin da Amurka
2013-11-22 15:59:21 cri
A ranar 21 ga wata, kasashen Sin da Amurka sun shirya taron tattaunawa a tsakanin manyan jami'an kasashen biyu game da musayar al'adu a karo na 4 tsakaninsu a birnin Wangshinton,domin ci gaba da inganta hadin gwiwa da gudanar da daidaiton da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu, a lokacin shawarwarin da suka yi a watan Yunin bana a wurin hutawa na Annenberg.

A lokacin tattaunawar mai taken "matasa da kirkiro da sabbin abubuwa" da Mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong da sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry suka shugabanta tare, shugabann kasashen biyu wato Mr. Xi Jinping da Barack Obama sun aika da sakon fatan alheri daya bayan daya.

Ban da wannan kuma, bisa sunan gwamnatocin kasashensu ne,Madam Liu Yandong da John Kerry suka rattaba hannu akan takardar fahimtar juna dangane da kafa tsarin yin musayar al'adu tsakanin manyan jami'an kasashen Sin da Amurka, sannan suka karanta jawaban su na fatan alheri inda a ciki suka waiwayi baya game da cigaban da aka samu bayan kafa tsarin tattaunawa tare da sakamakon haka,sannan kuma suka bada shawarar da a ci gaba da ba da gudummawa wajen ganin an cigaba da mu'amalar al'adu tsakanin kasashen biyu, don kafa sabuwar dangantakar a tsakanin manyan kasashen.

Haka kuma a lokacin taron bangarorin biyu sun yi shawarwari game da bangaren ilmi, kimiyya da fasaha, da al'adu da motsa jiki, da mata, da matasa na kasashen su, suka kuma waiwaiya baya game da aikin da ake yi cikin shekara guda da ta gabata, inda suka cimma daidaito daga fannoni 75 game da raya hadin gwiwa a tsakaninsu a nan gaba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China