Mista Hong wanda yake bayani ga manema labarai a ranar litinin din nan ya ce Kasar Sin tana lura da kokarin da kasashen Amurka da Farisa din ke yi kwanan nan domin inganta dangantaka tsakanin su ganin yadda Shugaban Amurkan Barrack Obama da na Farisan Hassan Rouhani suka tattauna ta wayar tarho a ranar jumma'an data gabata wanda shine karo na farko tsakanin shugabannin kasashen biyu tun juyin juya halin kasar Farisan sama da shekaru 30 da suka gabata.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ya ce wannan cigaba da aka samu tsakanin kasashen biyu yana da ma'ana ga ciyar da shirin sulhu a siyasance game da batun nukiliya na kasar Farisan gaba da kuma kokarin daidaita sauran batutuwa da suke kara rura wutan rikici.
Yace hakan yana da manufa mai kyau na cigaba da tabbatar da zaman lafiya a yankin.(Fatimah Jibril)