Yayin ganawarsu, Mr. Li Yuanchao ya bayyana cewa, a watan Yuni na wannan shekarar ce, shugabannin kasashen Sin da Amurka suka cimma ra'ayi daya kan kafa sabuwar dangantakar girmama juna da kuma cimma moriyar juna tsakanin kasashen biyu bisa fannoni daban daban. Kasar Sin tana fatan kara yin mu'amala da kasar Amurka, mutunta juna da kare manyan moriyar kasashen biyu, ta yadda za a karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu yadda ya kamata daga dukkan fannoni, karfafa mu'amalarsu kan harkokin kasashen biyu, shiyya-shiyya da kuma kasa da kasa, don shimfida aniyar girmama juna da kuma cimma moriyar juna cikin harkoki daban daban dake shafar gina dangantakar kasashen biyu.
A nasa bangare, Mr. Biden ya ce, dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka na da muhimmiyar ma'ana ga kasashen duniya. Kasarsa na dukufa wajen karfafa mu'amalar dake tsakanin shugabannin kasashen biyu, bunkasa hadin gwiwar kasashen biyu da kuma warware bambance-bambance dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata ba tare da boye kome ba, a kokarin inganta sabuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu. (Maryam)