Yanar gizon Intanet ta ma'aikatar tsaron kasar Sin ta ba da bayani a yau Juma'a ranar 13 ga wata kan tattaunawa karo na 14 tsakanin Sin da Amurka dangane da batun tsaro.
An ce, taron a wannan karo da aka yi a ran 9 ga wata an yi shi ne bisa jagorancin mataimakin hafsan-hafsoshin rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin Wang Guanzhong da mataimakin ministan tsaron kasar Amurka Miler tare.
Lafatana janar Wang Guanzhong ya bayyana fatansa ga Amurka na kiyaye zaman lafiya da karko a yankin Asiya da Pacific yayin da take daidaita tsarin da za ta dauka a wannan yanki. Ban da haka, ya jadadda cewa, batun Taiwan ya shafi moriya mai tushe na kasar Sin, hakan ya sa, Sin ba za ta ja da baya ko kadan kan wannan batu ba.
A nasa bangare, Miler ya furta cewa, Amurka na dukufa kan shawarwarin da ake yi tsakaninta da kasar Sin cikin dogon lokaci, da bunkasa dangantakar dake tsakanin sojojin kasashen biyu sosai. Amurka ba za ta goyi bayan yunkuri da za a yi domin ware yankin Taiwan daga kasar Sin ba, kuma ya ce, yana fatan babban yanki da Taiwan su kara tattaunawa domin warware wannan batu cikin lumana. (Amina)