Bisa labarin da aka bayar, an ce, kwamitin kula da tattalin arziki da tsaro na kasashen Amurka da Sin dake kasar Amurka ya gabatar da wani rahoto ga majalisar dokokin kasar a ranar 6 ga wata, inda ya bayyana cewa, babu alama da ke shaida cewa bangaren soja na kasar Sin ya daina kai hari ga internet ba.
Game da wannan batu, Hong Lei ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin na nuna adawa ga kai hari a kan internet, da yin kira ga kasa da kasa da su yi hadin gwiwa da gina yanayin internet mai zaman lafiya, tsaro, bude kofa da kuma hadin gwiwa. A lokacin da bullowar lamarin PRISM sa ido ga bayanan jama'a a kasar Amurka, idan har hukumomin kasar Amurka da abin ya shafa suna sha'awar cimma nasarar batun tsaron internet, sannan bai kamata kasar Amurka ta kyale lamarin, kuma ta fadi lamari na daban ba. (Zainab)