Tawagar kasar Amurka a taron, sun hada da sakatariyar cinikayya ta kasar Amurka Penny Pritzker, wakilin Amurka kan harkokin cinikayya Michael Froman da sakataren aikin gonan kasar Tom Vilsack.
A jawabinsa, mataimakin firaministan kasar Sin Wang Yang ya ce, yana fatan taron zai bunkasa kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu, matakin da shugabannin kasahen biyu suka cimma matsaya a kai, yayin taron kolin da suka yi a watan Yuni na bana a California.
Shi ma a jawabinsa, Mr. Froman ya ce, a yau sun bayyana kudurinsu na kawar da duk wasu shingayen cinikayya da zuba jari, tare da kara bude kofofin kawsuwaninsu, tabbatar da daurewar ci gaban dangantakar cinikayya da zuba jari tsakaninsu.
Sakatariyar cinikayya ta kasar Amurka Pritzker ta ce, gwamnati da shugabannin 'yan kasuwa da ke Anurka da duniya baki daya sun bayyana yadda hukumar hadin gwiwar kasashen za ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tare da daurewar shirin tsakanin kasashen biyu.(Ibrahim)