Wang ya ce, a bara a matsayin mataimakin shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya kai ziyara a ginin na Pentagon, wannan ya nuna muhimmancin da ya dora da kuma fatansa kan dangantaka tsakanin rundunar soja ta Sin da ta Amurka. A cikin 'yan shekarun da suka wuce, dangantaka tsakaninsu na samun kyautatuwa da bunkasuwa a kai a kai, hakan ya zama abin haske a fannin dangantaka tsakanin kasashen biyu. Dangantaka tsakanin rundunonin sojan kasashen biyu, wani muhimmin kashi ne na dangantaka tsakanin Sin da Amurka, kuma tsaro da amincewa da juna a fannin aikin soja, babban tushe ne na amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu. Kamata ya yi bangarorin biyu su dauki matakai su tabbatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, a kokarin kafa sabuwar huldar aikin soja dake dacewa da sabuwar dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu.
A nasa bangare, Charles Hagel ya yi farin ciki kan ci gaban da aka samu a fannin dangantaka tsakanin rundunonin sojan kasashen biyu, kuma yana sanya ran karfafa mu'amala da kara amincewa da juna da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin rundunar sojan Amurka da ta kasar Sin.
A wannan rana kuma, Wang Yi ya gana da tsoffin mataimakan shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaron kasa Thomas Donilon da Zbigniew Brzezinski.(Fatima)