Yayin da mista Yang yake ganawa da madam Susan Rice, mai ba da taimako ga shugaban kasar Amurka a harkokin tsaron kasa, ya bayyana cewa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin da shugaba Barack Obama na Amurka sun cimma muhimmin ra'ayi daya dangane da yadda Sin da Amurka za su kafa sabon salon hulda a tsakaninsu, sun kuma tsara manufar raya dangantakar da ke tsakanin kasashen 2 a nan gaba. Nufin gudanar da tattaunawa a karo na biyar tsakanin kasashen Sin da Amurka kan muhimman batutuwa da tattalin arziki shi ne fito da hakikanin matakai da manufofi kan aiwatar da wannan muhimmin ra'ayi da aka cimma. Sakamakon kokarin da kasashen 2 suka yi tare, ya sa aka samu muhimmin sakamako a yayin tattaunawar. Mista Yang ya yi fatan cewa, kasashen 2 za su ci gaba da kokarinsu na ganin, manyan jami'ansu sun kara yin cudanya da juna, kuma kasashen 2 sun inganta tuntubar juna ta fuskar muhimman batutuwa, kara amincewa da juna, hakaba hadin gwiwar da ke tsakaninsu, daidaita sabani yadda ya kamata, ta yadda za su raya huldar da ke tsakaninsu bisa hanyar da ta dace.
A nata bangaren kuma, madam Rice ta ce, shugaba Obama da gwamnatin Amurka ba za su karya alkawari kan yadda ake raya dangantaka a tsakanin Amurka da Sin ba. Suna himmantuwa wajen yin kokari tare da kasar Sin a fannin raya huldar da ke tsakaninsu ta hanyar daukar hakikanin matakai. Haka nan kasar Amurka ta yaba da sakamakon da aka samu a yayin tattaunawar.
Har wa yau a yayin da mista Yang Jiechi yake ganawa da ministan tsaron Amurka Chuck Hagel, ya bayyana cewa, kasar Sin na son hada kai da Amurka wajen ci gaba da inganta mu'amala a tsakanin sojojin kasashen 2, da kara amincewa da juna ta fuskar muhimman batutuwa, a kokarin kawar da gurguwar fahimtar juna a tsakaninsu ko yanke hukuncin da bai dace ba.
A nasa bangaren kuma, mista Hagel ya ce, Amurka za ta aiwatar da ra'ayi daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma a tsanake. Kuma bisa ga tattaunawar da aka yi a wannan karo, za ta kara yin tattaunawa, da mu'amala da hadin gwiwa da kasar Sin a harkokin soja, a kokarin zurfafa fahimtar juna da amincewa da juna, da kara raya dangantakar da ke tsakanin sojojin kasashen 2. (Tasallah)