Sin tana fatan za a fadada hadin gwiwar samun moriyar juna a tsakaninta da kasar Amurka
Game da taron hukumar hadin gwiwar kasashen Sin da Amurka kan harkokin ciniki da za a gudana a nan birnin Beijing na kasar Sin, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a ranar 17 ga wata cewa, kasar Sin tana fatan kasar Amurka za ta sassauta manufofinta na kayyade fitar da kayayyakin fasahohin zamani daga Amurka zuwa Sin, da nuna adalci ga kamfanonin Sin da za su zuba jari a kasar Amurka, kara hadin gwiwa wajen daukar matakan tabbatar da ikon mallakar fasaha, da kuma kara yin kokari tare da kasar Sin wajen fadada hadin gwiwarsu ta samun moriyar juna.
Za a gudanar da taron hukumar hadin gwiwar Sin da Amurka kan harkokin ciniki karo na 24 tun daga ranar 19 zuwa 20 ga wata a nan birnin Beijing, inda mataimakin firaministan kasar Sin Wang Yang da sakatariyar harkokin ciniki ta kasar Amurka Penny Pritzker da kuma wakilin kasar Amurka mai kula da harkokin ciniki Michael Forman za su shugabanci taron. (Zainab)