Kafin ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, mista Wang ya bayyana ma manema labaru cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama sun gana da juna karo 2 cikin watanni 3 a bana, inda suka cimma matsaya daya kan kokarin raya huldar dake tsakanin manyan kasashen 2. Don haka a wannan karo, ya kai ziyara kasar Amurka, don neman aiwatar da matsaya daya da shugabannin 2 suka cimma, ta yadda za a samu damar kyautata huldar dake tsakanin Sin da Amurka bisa wasu hakikanan matakan da za a dauka.
Yayin da mista Wang yake ganawa da mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden. Mista Biden ya ce, ci gaban kasar Sin ya dace da moriya kasar Amurka, da kuma moriyar bai daya ta kasashen duniya, a don haka yana sa ran ganin ci gaban huldar dake tsakanin kasashen Amurka da Sin. (Bello Wang)