Rajiv Biswas, babban masani a fuskar tattalin arziki na reshen Asiya da tekun Pacific na wata hukumar nazarin harkokin tattalin arziki ta kasar Amurka wato "IHS Global Insight" ya bayyana cewa, ra'ayin da aka bayar kan cewa wai kasar Sin na samun tabarbarewar tattalin arziki ba ya da tushen gaskiya. A hakika dai, bisa kiyasin da hukumar ta yi, an sheda cewa, tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da samun saurin bunkasuwa. A cewar mista Biswas, ko da yake yawan bukatun kasar Sin na fitar da kayayyakinta zuwa kasashen ketare ya ragu, ta yadda yawan kayayyakin da wasu muhimman masana'antun kamar sana'ar samar da karfe suka samar ya yi yawa fiye da kima, amma sakamakon karfin zuciya da masu sayayya ke nunawa, da kuma wasu manufofin da gwamnatin kasar Sin ta fitar domin taimakawa ci gaban tattalin arziki, an yi kiyasta cewa, jimillar karuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekara ta 2013 za ta kai kashi 7.5 cikin dari.(Kande Gao)