An bude taron tattaunawa karo na 5 tsakanin shugabannin masana'antu da tsoffin jami'an gwamnati na kasashen Sin da Amurka
A ranar 21 ga wata, a birnin Washington hedkwatar kasar Amurka, an bude taron tattaunawa karo na 5 tsakanin shugabannin masana'antu da tsoffin jami'an gwamnati na kasashen Sin da Amurka da za a shafe kwanaki biyu ana yinsa, tsohon firaministan kasar Sin kuma shugaban cibiyar mu'amalar tattalin arziki ta kasa da kasa ta kasar Sin Zeng Peiyan da shugaban hukumar kasuwanci ta kasar Amurka Thomas J. Donohue, da shugabannin masana'antu na kasashen biyu, tare da tsoffin jami'ansu, da ma shahararrun masana da dama sun halarci bikin bude taron.
Yayin da Zeng Peiyan ke yin jawabi a gun bikin fara taron, ya ce, za a tattauna batun kyautata yanayin saka jari dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, da sa kaimin saka jari kan muhimman ababen more rayuwa a tsakanin kasashen Sin da Amurka da ma sauran fannoni. Ya kuma bayyana cewa, sakamakon yadda take dora muhimmanci kan taron, bangaren Sin zai kuma gabatar wa mahalarta taron yanayin da ake ciki a yankin yin kasuwanci cikin 'yanci na birnin Shanghai.
A nasa bangare, shugaban hukumar kasuwanci ta kasar Amurka Donohue ya bayyana cewa, makasudin shirya wannan taro shi ne karfafa dangantakar bangarorin biyu, wadda ke da muhimmanci sosai.(Bako)