in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayyana fatan samun ci-gaba a dangantakarta da kasar Amurka
2013-12-03 20:12:32 cri
Yayin da mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden ke shirin kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 4 zuwa 5 ga watan Disamba, kasar ta Sin ta bayyana fatan samun ci-gaba a dangantakar da ke tsakaninta da kasar ta Amurka.

Kakakain ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan kara yin kokari da Amurka wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma kan bunkasa wata sabuwar dangantaka da ba nuna tashin hankali, tsukana da mutunta juna da cin moriya tare.

Hong Lei ya ce, kamata ya yi kasashen biyu, su kara amincewa da juna, warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu kana da hanzarta bunkasa sabuwar dangantakar da ke tsakaninsu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China