Yayin ganawar, shugaba Xi ya bayyana fatan cewa, ziyarar da Biden din ke yi za ta kara karfafa amincewa da juna, yin musaya da hadin gwiwa tsakanin ksashen biyu.
Ya ce, yayin da ake fuskantar canje-canje masu sarkakiya a duniya, kamata ya yi Sin da Amurka kasancewarsu manyan kasashe masu karfin tattalin arziki kana kasashe masu kujerun din-din-din a MDD su dauki nauyin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya tare da bunkasa ci-gaba.
A shekara mai zuwa ne za a cika shekaru 35 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Amurka, inda shugaba Xi ya lashi takwabin hada karfi da karfe da Amurka kan mutunta muradun juna da muhimman batutuwa da ke shafarsu, bunkasa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare kan batutuwan duniya da na shiyya-shiyya, daidaita batutuwa masu sarkakiya da bambance-bambancen da ke tsakaninsu don tabbatar da samun bunkasa tsakanin sassan biyu.
A yau da safe ne Mr. Biden ya iso birnin Bejing, don ziyarar aiki ta yini biyu, kuma wannan ita ce ziyararsa ta biyu zuwa nan kasar Sin a matsayinsa na mataimakin shugaban kasar Amurka.(Ibrahim)