Lokacin tattaunawa da mataimakin shugaban kasar Amurka da yake ziyara yanzu haka, kasar ta Sin ta jaddada daukan wannan matakin a tekun gabashin kasar ADIZ tana mai bayyana hakan da cewa yana bisa doka da kuma abin da aka saba gani a sauran kasashen duniya.
A cikin sanarwar, Mr. Hong ya bayyana cewa, shugabannin kasar Sin da mataimakin shugaban kasar Amurkan sun tattauna sosai kuma sun yi nazari mai zurfi a kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da sauran batutuwan da suka fi jawo hankalinsu a lokacin ziyarar Mr Biden. (Fatimah)