Minista mai kula da harkokin hanyoyin kasar Ghana Alhaji A.B.Inusah Huseini ya bayyana cewa, Ghana na maraba da kamfanonin kasar Sin da daidaikun mutune masu zuba jari na kasar da su shiga ayyukan gina manyan ababen more rayuwa da suka hada da hanyoyin mota, hanyoyin dogo da dai sauransu.
Yayin da yake zantawa da manema labaru a nan birning Beijing , Malam Huseini ya ce, ziyararsa kasar Sin a wannan karon na da nufin tabbatar da yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin kimiyya da fasaha ta fuskar tattalin arziki, da neman kyautata hanyoyin kasar ta samar da rancen kudi cikin gatanci. Ya kuma kara da cewa, yanzu gwamnatin kasar Ghana na tsara wasu manyan ababen more rayuwa ciki hadda hanyoyi masu saurin tafiya da sauransu, don hakan tana fatan masu zuba jari daga kasashen Sin Amurka da EU da sauransu su nuna himma da gwazo don shiga ayyukan gina wasu manyan ababen more rayuwa kamar su hanyoyin motoci da hanyoyin dogo, ita kuma a nata bangare, kasar ta Ghana zata samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari a wannan fanni. (Amina)