in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta taimakawa kasar Ghana wajen raya sha'anin karatu daga gida
2015-02-03 10:54:44 cri
A kwanakin baya ne, aka yi bikin mika kashi na biyu na aikin raya sha'anin karatu daga gida na jami'ar Ghana da kamfanin Unigroup na Tsinghua na kasar Sin ya gudanar a kwalejin ilmi ta jami'ar dake birnin Accra.

Kashi na biyu na aikin raya sha'anin karatu daga gida na jami'ar Ghana ci gaba ne na farko, wanda ke tsagayoyi 12 na jami'ar Ghana da ke fadin kasar, don hade su da na'urorin koyarwa na bai daya tare da samar masu wani tsarin manhajar karatu.

Rahotanni na cewa, ta wannan hanya, za a inganta sha'anin bada ilmin zamani na kasar Ghana zuwa wani sabon matsayi, kana za a rage gibin dake tsakanin kasar da kasashe masu ci gaba na duniya a wannan fanni.

Wani babban jami'i a jami'ar ta Ghana ya bayyana cewa, wannan hanya ta sa jami'ar Ghana ta samu tsarin karatu daga gida na zamani, ta haka za a kara samar da damar samun ilmi ga dalibai bisa tushen tabbatar da ingancin bada ilmi. Jakadar Sin dake kasar Ghana Sun Baohong ta bayyana cewa, fannin bada ilmi muhimmin fannin hadin gwiwa ne a tsakanin Sin da Ghana, ba ya ga samar da taimakon gina kayayyakin more rayuwa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da samar da taimakon guraben karo ilimi ga daliban kasar Ghana da su zo kasar Sin su yi karatu.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China