An ce, kafin rukunin ya tashi, an horar da masanan uku a kasar Sin game da matakan rigakafi da yaki da cutar Ebola a kasar Ghana da kuma fasahohin gudanar da horaswa a yankunan da ke fama da cutar. Daya daga cikin masanan uku ya bayyana cewa, za su yi hadin gwiwa da tawagar likitocin Sin dake kasar Ghana da ma'aikatar kiwon lafiya ta Ghana don horar da likitoci a kalla 500 a cikin wata guda.
A farkon watan Nuwanba na shekarar 2014 ne rukunin farko na malaman bada ilmin kiwon lafiya na kasar Sin ya fara aikin horaswa a kasar Saliyo. Ya zuwa yanzu an gudanar da irin wannan aiki a kasashen Liberia, Guinea, Mali, Ghana, Benin, Togo, Senegal, Guinea Bissau da dai sauransu, kana yawan likitoci da ma'aikatan kiwon lafiya da ke unguwoyi da aka horar ya kai fiye da dubu daya. (Zainab)